18 Afirilu 2026 - 21:31
Source: ABNA24
Pakistan: An Warware Batun Takunkumai Da Kadarorin Iran Da Aka Rike

Ministan Harkokin Wajen Pakistan: An Warware Batun Takunkumai Da Kadarorin Iran Da Aka Rike A Tattaunawar Islamabad

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Mataimakin firaministan kasar Pakistan kuma ministan harkokin wajen Pakistan ya yi ikirarin cewa an warware batutuwan takunkumin Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da warware batun kadarorin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a zagayen farko na tattaunawar Islamabad. 

Sanata Mohammad Ishaqdar ya fada a cikin wata sanarwa a wani taron Majalisar Diflomasiya ta Antalya cewa an warware batun takunkumi da kuma toshe kadarorin Iran a tattaunawar Islamabad. 

Your Comment

You are replying to: .
captcha